1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin samar da rigakafin Covid-19 a Jamus

April 23, 2020

Cibiyar Paul Ehrlich Institute da ke Jamus ta bayar da damar a fara gwajin rigakafin coronavirus a karon farko a kasar. Ana sa ran za a yi gwajin rigakafin cutar a kan mutane kafin karshen watan  Afrilu. 

Deutschland Berlin Coronavirus - Pressekonferenz Angela Merkel
Hoto: picture-alliance/AP/M. Schreiber

Cibiyar ta ce tana sa ran za ta kammala gwajin a karshen watan Yuni.  A yanzu Jamus ta shiga sahun kasashen da ke baje basirarsu ta kimiyya don samo ma duniya rigakafin corona cutar zamani.


Wannan na zuwa ne a yayin da a Alhamis din nan Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel a yayin jawabin da ta yi wa 'yan majalisar dokokin kasar ta Bundestag, ta ce Jamus za ta ci gaba da bayar da gudunmawar kudi ga kungiyar Tarayyar Turai ta EU don yaki da coronavirus. Kazalika Merkel ta yi amfani da damar wurin fadin ra'ayin kasar Jamus a kan ayyukan hukumar lafiya ta duniya, WHO. 


''Ba wai nahiyar Afirka kadai ba ce ta dogara ga ayyukan WHO. A madadin gwamnatin Jamus ina kara jaddada cewa WHO abokiyar tafiya ce ga Jamus a yaki da coronavirus kuma muna goyon bayan ayyukanta.'' inji Merkel


Jawabin na Merkel dai na zuwa ne wasu 'yan awanni kafin tattaunawar da aka shirya gudanarwa a tsakanin mambobin kungiyar EU a kan yadda za a ceto kasashen Turai daga radadin annobar coronavirus wace ta ragargaza tattalin arzikin duniya.