Najeriya: Buhari ya kulle Kano
April 28, 2020Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari dai, ya fito ne da nufin kwantar da hankalin al'ummar Tarayar Najeriyar da idanuwansu ke dada budewa da barazanar annobar mai tasiri a cikin kasar. Tun ba a kai ga ko'ina ba dai al'ummar sun fara mayar da martani ga jawabin da ya ambato sassautawa a biranen Legas da Abuja da jihar Ogun, sannan da kara tsaurin matakai a jihar Kano da ke neman rikidewa ya zuwa cibiya ta cutar a kasar.
Kyakkyawan fata
Faruk B B Faruk na zaman wani mai sharhi a cikin harkokin mulki na kasar, ya kuma ce tsarin da shugaban kasar ke dauka na kama da kwaiwayon Turawan da ke da arziki na tunkarar annobar a cikin sauri. Ga Hashim Sule da ke shirin tunkarar wasu makonni guda biyu a birni na Kano, akwai sabon fata a kalaman shugaban kasar.
Ra'ayi dai ya bambanta tsakanin likitoci da ke tunanin karbe yakar cutar a hannun gwamnatin jihar da kuma masanan da ke ganin a kyale gwamnan ya taka rawa, na iya tasiri a kokari na tunkarar rikicin.
Hada hannu ko karbewa?
Dr. Husaini Tukar Hassan na zaman wani masani a cikin harkokin mulki, a cewarsa akwai bukatar shugaban kasar ya hada hannu da gwamnatin jihar domin warware batun. To sai dai ga Dr. Mohammed Adamu Askira da ke zaman wani likita a Kanon, karbe yakin daga hannu na jihar kadai ne zai iya taimakawa wajen kaucewa tunkarar annoba mai girma
Ya zuwa ranar yau dai yawan masu dauke da cutar ya tasamma 1,500 a daukacin Najeriyar, a yayin kuma da asara ta rayuka ta kai 40.