Kasashe na neman mafita kan cutar corona
April 14, 2020Kasashe a fadin duniya na fafutkar samun mafita ga koma bayan tattalin arziki da karuwar rashin aikin yi a sakamakon killacewar da aka yi saboda cutar COVID 19.
A wasu yankuna na Amirka da nahiyar Turai ana kallon takardar shaidar samun garkuwar jiki da kariya daga COVID 19 tare da gwajin magani a matsayin wata hanya ta kawo karshen killacewar ba shiga ba fita domin bai wa jama'a damar komawa bakin aiki.
Sai dai kwararru na gargadin cewa mai yiwuwa gwamnatocin sun yi gaggawa.
Kasar Austria ita ce ta farko da ta dauki matakin sassauta tarnaki yayin da ake sa ran a gobe Laraba shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta sanar da bude wasu shaguna da kuma mai yiwuwa bude makarantu karkashin tsauraran dokoki.
Hatta kasashen Spaain da Italiya inda cutar ta fi kamari da haddasa mutuwar jama'a suna shirin yadda za su kawo wa al'umominsu saukin matsin tattalin arziki da kuma damuwa.