1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta taimaki EU kan COVID-1

Abdullahi Tanko Bala LMJ
April 23, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ja hankali da cewa duk da alamun nasarar da ake gani an fara samu a yaki da annobar Coronavirus, bai kamata a yi kasa a gwiwa ba.

Angela Merkel Rede an die Nation zur Corona-Krise Berlin Bundestag
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: Reuters/A. Schmidt

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi ga 'yan majalisar dokoki a birnin Berlin, gabanin wata muhimmiyar tattaunawa da shugabannin Tarayyar Turan za su yi kan gagarumin shirin tallafin ceto na Tarayyar Turan, batun da ya sake haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin kasashe masu arziki da kuma matalauta.

Wajibi ne a takaita harkoki

Kudirin gwamnati na takaita harkokin hada-hadar jama'a sakamakon barkewar annobar Coronavirus, mataki ne da ya zamanto tilas babu wani zabi a cewar shugabar gwamnatin.

Merkel ta yi jawabi ga majalisaHoto: Reuters/A. Hilse

Matakan dai su bai wa Jamus damar kaucewa ta'azzarar cunkoson marasa lafiya a asibitoci, kamar yadda kaddara ta fadawa kasashen Faransa da Italiya a farkon barkewar annobar. Sai dai kuma shugabar gwamnatin Jamus din, ta ja hankali da a yi taka tsan-tsan yayin da ake komawa harkokin rayuwa na yau da kullum. Merkel ta kuma yi kira ga 'yan majalisar dokoki da al'ummar Jamus su kara hakuri su kuma nuna da'a da bin doka da oda domin kaucewa durkushewar tattalin arziki, yayin da ake dokin komawar al'amuran rayuwa.
 
Matakin taimakon juna

Shugabar gwamnatin ta kara da cewa halin da aka shiga na yaki da annobar corona zakaran gwajin dafi ne ga Tarayyar Turai. Ta ce nahiyar Turai ba za ta kasance tarayya ba, har sai sun taimakawa juna a lokacin tsananin bukata da kuma a lokacin wahala.

Coronavirus ta janyo asarar rayukaHoto: picture-alliance/dpa/A. Calanni

Ta ce za su samar da shirin tallafi domin taimakawa farfado da dukkanin fannoni na rayuwa cikin shekaru biyu masu zuwa, wannan shi ne abin da suke aiki a akai tana mai cewa: "Mun kasance tare kuma aminan juna da zuciya daya, ya kamata mu kara tabbatar da haka a hali na rashin tabbas da kalubalen annoba, mu kasance al'umma daya kuma tarayyar turai guda daya."

Ga hukumar lafiya ta duniya Merkel ta ce babbar abokiyar tafiya ce, kuma suna taimaka musu domin cimma kudirin da suka sanya a gaba ta lafiya a duniya baki daya. A wannan Alhamis din ne dai shugabannin kasashen Turan 27, suke gudanar da taro domin nazarin illoli da kuma tasirin da cutar Coronavirus din ta yi ga tsarin lafiya na Tarayyar Turai da kuma rayuwar mutane kusan miliyan 500 a fadin nahiyar, inda kuma ake sa ran za su amince da kasafin kudi Euro biliyan 540 na agajin gaggawa, domin farfado da harkokin tattalin arzikin Tarayyar Turai.