Najeriya ta yi sammaci ga jakadan Chaina
April 14, 2020Ministan kula da harkokin kasashen wajen Najeriya ne ya bayyana haka a Abuja, yayin ganawa da jakadan kasar Chainan a Najeriya a ofishinsa.
Cikin wani faifen bidiyo da aka yi ta yadawa a kafofin sada zumunta da ma na talabijin na Najeriyar ne dai, aka nuna yadda jami'an kasar Chainan ke fizge takardar fasfo daga hannun 'yan Najeriyar ana kuma hantararsu, tare da tasa keyarsu daga gidajensu, a wani mataki na yaki da cutar ta Coronavirus a birnin Guangzhou na kasar ta China.
Neman ba'asi daga Chaina
Wannan lamarin dai ya daga hankalin mahukuntan Najeriyar, abin da ya sanya ministan kula da harkokin kasashen ketare na Najeriyar Geoffrey Onyeama ya gana da jakadan Chaina a kasar,domin neman ba'asi.
A nasa bangaren, jakadan kasar ta Chaina a Najeriyar Mr. Zhou Pingjian ya amsa kiran, inda suka gana da ministan a kan wannan lamari, inda ya musanta batun cin zarafin 'yan Najeriyar a kasarsa.
Najeriya ta gamsu
Tuni dai wannan lamari ya janyo mayar da martani da bukatar daukar mataki, ganin cewa Najeriyar ta ce ta gamsu da bayansa. Su ma dai masu fafutukar kare hakin dan Adam, irin su Comrade Isa Tijjani sun e za su zuba idanu su gani. Sake fuskantar takaddama a kan wannan batu tsakanin Najeriya da Chaina dai, abu ne da ke daukar hankali ganin yadda Chainan ke kara samun tasiri a Najeriyar da ma kasashe da dama na Afirka.