1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An baiwa cutar Coronavirus suna

Binta Aliyu Zurmi
February 11, 2020

A yau Talata hukumar lafiya ta duniya ta ba wa cutar numfashi ta Coronavirus suna, wanda ta ce daga yau sunan cutar COVID 19.

China Wuhan Augenarzt  Li Wenliang gestorben
Hoto: Weibo

A sanarwar da ya rabawa manema labarai a Geneva, shugaban hukumar  Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce "CO" a matsayin Corona "VI" a matsayin Virus sai "D" kuma a matsayin Dieseas watau cuta 19 kuma a matsayin shekarar da cutar ta bullo. Shugaban hukumar ya ce sun samar da wannan sunan ne domin kauce amfani da sunan Corona da ke da alaka da mutane da dabobbi dama yankuan wasu alumma.

Bugu da kari Ghebreyesus ya ce duniya ta dauki cutar a matsayin wata babbar makiyar kowa da kowa. Ya zuwa yanzu dai sama da mutum dari ne suka mutu sanadiyar cutar yayin da wasu da dama suka kamu da ita. An sa ran a nan da watanni goma sha takwas a samo maganin wannan annobar da ke nema ta zama ruwan dare gama duniya.