Saudiyya: Annobar corona ta takaita aikin Hajjin bana
June 23, 2020Hukumomi a Saudi-Arabiya sun fidda sanarwar cewar maniyata aikin Hajjin bana daga kasashen ketare ba za su samu damar yin aikin hajji ba saboda halin da ake ciki na annobar coronavirus. Sai dai hukumomin kasar sun ce 'yan kasar ta Saudiyya da kuma baki masu zama a kasar ne kawai ke da damar yin aikin hajjin bisa wasu sharudda da ta gindaya.
Wannan matakin da hukumomin Saudiyya suka dauka na zuwa ne a daidai lokacin da aka jima a na kila wa kala kan batun aikin hajjin wannan shekarar biyo bayan da hukumomin kasar suka ambaci cewar ba su karbi kudaden aikin hajjin ba daga al'ummomin kasashen ketare.
Domin magance matsalar yaduwar annobar coronavirus a aikin hajjin Saudiyya ta za ta kiyaye wasu sharuda na takaita jama'a, saka motocin dokar maniyata, yi masu feshen maganin kashe kwayoyin cutar coronavirus ga jama'a.
Tuni masu shirya tafiye-tafiyen aikin Hajji a wannan shekara na cigaba da bayyana takaicinsu bisa wannan mataki da hukumomin Saudiyya suka dauka wanda suke cewar ya zam wata babbar barazana ga tattalin arzikinsu. Haka suma al'ummar Musulamai maniyata na ci gaba da kasancewa cikin rashin jin dadi kan matakin Saudiyya.