1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Corona: Trump ya yi alkawarin samar da rigakafi

November 14, 2020

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba zai sanya dokar kulle a kasar ba, komai kuwa zai faru a dangane da annobar coronavirus.

Washington | Präsident Trump Statement Operation Warp Speed
Hoto: Mandel Ngan/AFP/Getty Images

Mr. Trump ya sanar da haka a yayinda ya yi fitowa ta farko a bainar jama'a tun bayan sanar da kayar da shi a zaben kasar da ya gabata.


Wannan matsaya ta shi na zuwa ne a yayinda coronar ta halaka mutum 1,300,000 a cikin mutane 53,000,000 da ta kama a sassa daban-daban na duniya. Kwararru na kira ga Amirka da ta kara daukar mataki domin coronar ta halaka mutum sama da 240,000 ta kuma kama mutum 10,000,000 a kasar. To amma Donald Trump ya ce duk matakin da za a dauka babu maganar sanya dokar kulle, yana mai alkawarin cewa za a samarwa da Amirka rigakafin cutar daga nan zuwa watan Afrilu mai zuwa.