'Yan Najeriya na kokawa da zaman gida
March 26, 2020Tun daga farkon makon nan ne dai gwamnatoci a matakan tarayya da jihohi suka umarci ma'aikata da sauran al'umma da su koma gida, a wani abin da ke zaman matakin dakile cutar da ke ta kara yaduwaa ko'ina cikin kasar. To sai dai kuma kama daga ma'aikatan gwamnati ya zuwa ragowar mazaunan gari, tuni hutun ya fara gundurar rayuwa da ma tauye tattali na arziki. Aliyu Bala dai na zaman wani ma'aikaci a Abuja, da kuma ya ce ya koma daukar saitin inuwa da nufin rage radadin hutun dolen da ya fada.
Rashin Internet da hasken wutar lantarki
In har wasu na neman hanyar tserewa yara, ga wasu ma'aikatan kamar Aliyu Mudi batun rashin wuta na zaman matsalar da ke barazana ga gudanar da aikin a gida kamar yadda masu mulkin Tarayyar Najeriyar ke fata su gani. Ko bayan karanci na wuta dai, kasar na kuma fama da rashin isasshen tsari na Internet da ke iya taimakawa masu takama da yin aikin a gida cimma buri.
Duk da takama da arziki dai kusan biyu cikin uku na 'yan kasar na dogaro da ci da guminsu, kafin iya kai wa ga warware matsaloli na rayuwa. Halin yau da ma tunanin gobe na neman cusa da daman al'ummar Tarayyar Najeriyar cikin wani yanayi, inda mafi yawansu ke rayuwar hannu baka hannu kwarya.
Da yawa sun kosa da hutun
Tuni dai hutun ya fara taba irin su Hashim Suleiman da ya ce akwai matsala babba ga kokari na samar da na baki na salati. Ma'aikata dai na shirin shafe makonni hudu a killace da fatan tura Coronavirus zuwa kabari, a yayin da kannensu da ke a jihohi ke shirin share makonni tsakanin biyu zuwa hudu cikin sabon yakin.