1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Ma'aikata za su zauna gida saboda Coronavirus

Abdourahamane Hassane
March 13, 2020

Gwamnatin Jamus ta amince da wasu dokoki da ke ba da dama ga kamfanoni da sauran ma'aikatu na takaita adadin ma'aikata a wuri aiki domin rage yawan cunkoso da ka iya zama hadari na kamuwa da cutar Coronavirus.  

Budesliga | Bayern München vs 1. FC Köln  - Mats Hummels und Anthony Modeste
Hoto: Getty Images/AFP/C. Stache

Za a rika biyan kudaden albashi ga ma'aikata ko ba su je aiki ba, gwamnatin ta Jamus ta ce za ta tallafa wa kamfanoni da kudaden bashi domin rage asarar da suke yi a sakamakon cutar ta Coronavirus.

A waje guda hukumar wasanin kwallon kafar ta Jamus  DFL ta dakatar da wasanin Bundesliga har zuwa ranar biyu ga watan Afrilu.