1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Corona na ci gaba da yaduwa a Turai

Binta Aliyu Zurmi
February 26, 2020

Babbar jami'ar da ke kula da harkokin lafiya a kungiyar Tarayyar Turai, Stella Kyriakides ta yi kira ga kasashe mambobin kungiyar da su hada kai wajen samar da sahihan bayanai a tsakaninsu kan annobar Coronavirus.

Stella Kyriakides
Hoto: Reuters/Y. Herman

Wannan kira na zuwa ne a lokacin da suka gana da manema labaru a birnin Roma na Italiya tare da ministan lafiyar kasar, inda cutar ke ci gaba da yaduwa. Babbar jami'ar ta EU ta kuma bukaci mutane su kwantar da hankali, tana mai cewa nan gaba kadan za a fidda bayanai ga matafiya musamman a kan wannan cuta.

Annobar da ke kara yaduwa a nahiyar Turai, a yanzu kasashen Spain da Girka sun sami sabbin wadanda suka kamu. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya ke cewar sabbin wadanda suka kamu da cutar a sauran sassa na duniya sun zarta yadda suke a Chaina.