1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Ebola na ci gaba da daukar hankalin jaridun Jamus

September 5, 2014

Yayin da nahiyar Afirka ke neman hanyoyin shawo kan cutar Ebola jaridun Jamus sun yi sharhuna masu yawa game da wannan cuta.

Ebola in Liberia (Behandlung im Krankenhaus)
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Mujallar Der Spiegel ta ce aikin tsaida cutar ta Ebola bai tsaya kan kasashen Afirka, ko kuma hukumar lafiya ta duniya kadai ba. Kasashe masu ci gaban masana'antu tilas su ba da gudummuwarsu. Jami'in kungiyar likitocin duniya, Brice de le Vigne ya ce ana bukatar taimako na gaggawa daga kasashen da suka ci gaba, saboda ita kanta Hukumar Lfiya ta Duniya sai da aka makara sa'annan ta tashi tsaye game da yaki da cutar, saboda tun cikin watan Aprilu aka san cewar barkewar Ebola a wannan karo, ba kamar yadda aka saba gani ba a shekarun baya.

Ita kuwa jaridr Süddeutsche Zeitung tayi sharhi ne da cewar: bisa al'ada, idan mutum ya kamu da rashin lafiya ya kan sha magani domin ya warke, to sai dai a game da cutar Ebola, ko shan magani kadai zai isa kawar da ita baki daya? A tsakiyar mako, mukaddashin janar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Jan Eliasson dake jawabi a New York, ya kwatanta Ebola da bala'in Tsunami da ta aukawa Asiya shekaru 10 da suka wuce. Yayi tambayar: shin magani zai iya tsayar da Tsunami? Cutar Ebola yanzu dai tana ci gaba da yaduwa ba ma a kasashen Afirka ta yamma kadai ba, amma har tana neman mamaye Afirka baki daya. Lokaci yayi da duniya gaba daya zata tashi tsaye domin yaki da cutar, abin da ba ma Jan Eliasson yake ganin dacewar haka , amma har da darektan Hukumar Kwon Lfaiya ta Duniya, Margaret Chan, wadda aka sha zargin hukumarta da jan kafa a matakan shawo kan cutar ta Ebola.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta tabo batun hare-haren da Amirkawa ne suka kaiwa kungiyar Al-Shabaab a Somaliya. Jaridar tace ko da shike shugabanni a ma'aikatar tsaron Amirka a Washington sun ki tabbatar da wannan hari, amma rahotanni sun gasgata cewar jiragen saman yakin Amirkan sun aukawa jerin gwanon motocin yan kungiyar Al-Shabaab, inda ma har suka sami nasarar kashe shugaban kungiyar, wato Ahmed Abdi Godane. Gwamnan lardin Lower Shabelle, Abdikadir Mohammed Nur Sidii yace jiragen Amirka masu tuka kansu, sun kai hari kan yan kungiyar ta Al-Shabaab, inda suka sami nasarar kashe shugabanta. Wannan kungiyar dai ita ce ake zargi da laifin hare-haren ta'addanci a yankunan Afirka ta gabas, ciki har da mummunan harin nan kan cibiyar ciniki ta Westgate birnin Nairobi a bara, inda akalla mutane 67 suka mutu. Wannan mataki na Amirka, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ya zama abin dakie nuna yadda Amerika ta lashi takobion kawo karshen aiyukan ta'addanci a nahiyar Afirka. Hakan ma shi ya sanya Washington take kokarin kafa sabon sansani na mayakanta a yankin Agadez na arewacin Niger.

Hoto: M:Abdiwahab/AFP/Getty Image

A Mozambik a karshen wannan mako za'a fara kampe na neman kuri'u a zaben shugaban kasar da zai gudana ranar 15 ga watan Oktoba. Jaridar Tageszeitung tace shugabannin jam'iyu biyu dake gaba da juna, wato Alfonso Dhlakama na jam'iyar Renamo da shugaban kasa Armando Guebuza na jam'iyar Frelimo, sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya da nufin gudanar da wannan kampe cikin kwanciyar hankali. An shirya Dhlakama zai fito daga maboyarsa a dajin Gorongoza, domin saduwa da abokin adawarsa, Guebuza, inda za su sanya hannu kan yarjejeniyar da mashawartansu suka cimma ta zaman lafiya. Hakan zai sanya kyakkyawan fata a zukatan yan Mozambik masu yawa game da samun tabbataccen sulhu a wannan kasa.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Suleiman Babayo