Cutar Ebola ta kama mutum na uku a kasar Kenya bayan kashe biyu
October 16, 2026
An samu mutum na uku da ya kamu da cutar Ebola a Kenya, mace ce, kuma 'yar uwa ce ga mutane biyun farko da suka fara kamuwa da ita, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta kasar ta sanar a wannan Juma'a.
Karin bayani: Adadin masu fama da Ebola a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango ya haura 8,000
Tuni hukumomin lafiyar kasar suka killace matar mai shekaru 65, tun ranar shida ga wannan wata na Oktoba da mu ke ciki, bayan ta fara nuna alamun cutar, sanadiyyar zazzabi da ciwon makogwaro da kasala.
Karin bayani: Ana samun haske a yaki da cutar Ebola a Kwango-WHO
Mako guda ke nan da aka samu mutum na biyu a Kenya da cutar ta kama, kuma 'dan uwa ga wannan tsohuwa, haka zalika dukkansu 'yan uwa ga mutum na farko da ta ya taba kamuwa da Ebola a tarihin Kenya.
Karin bayani:Kwango ta fara bai wa ma'aikatan jinya rigakafin cutar Ebola
Tuni dai cutar ta halaka mutum na farkon, wanda a baya ya yi zama a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, kafin daga bisani ya koma kasarsa ta asali Kenya, inda bincike ya tabbatar da kamuwarsa da cutar, daga bisani rai ya yi halinsa.
Karin bayani: Hayar yanzu akwai sauran aiki a yaki da Ebola
Tun cikin watan Mayun 2026 annobar cutar Ebola ta barke a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, karo na 17 a tarihinta, wadda ta kashe mutane fiye da 15,000 a cikin shekaru 50.
Idan aka hada da mutane 9,066 da suka kamu a 2026, sai 4,381 da ta yi ajalinsu.