1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Ebola ta tabbata a kasar Kwango

August 25, 2014

Hukumomin Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango sun tabbatar da bullar cutar Ebola wadda tuni tayi sanadiyar rasuwar mutane 13 a wannan kasa.

Hoto: picture-alliance/dpa

Hukumomi a Kinshasa suka ce cuta Ebola ta bulla ne a yankin Arewa maso Yammacin kasar ta Kwango. Ministan kiwon lafiyarkasar Félix Kabange Numbi ya ce babu shakka sakamako sun tabbatar cewa cutar Ebola ce wadda tuni tayi sanadiyar mutuwar mutane 13 tun daga ranar 11 ga watan nan na Agusat a yankin Equateur. Sai dai kuma Ministan kiwon lafiyar kasar ta Kwango, ya ce wannan kwayar cuta ta Ebola ta sha bamban da wadda ke wakana a yammacin nahiyar Afirka.

A nata bangaren, Hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da kamuwar daya daga cikin kwararrun ma'aikatanta da cutar ta Ebola a kasar Saliyo, inda hukumar tace wannan shi ne karo na farko da wani daga cikin ma'aikatanta akalla 400 dake ayyukan agaji a inda ake fama da cutar ya kamu da ita.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe