Ebola ta yi wasan baya a Kwango
September 5, 2018Talla
Garin na Butembo da ke da yawan al'umma kusan miliyan guda, na da kan iyakoki da Yuganda abin da ke janyo wahala ga yunkurin dakile yaduwar cutar, kamar yadda mahukuntan kasar suka tabbatar. Rahotanni sun nunar da cewa daga watan Yulin wannan shekara kawo yanzu, mutane 85 ne suka hallaka sakamakon cutar ta Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon, yayin da wasu 39 suka kamu da ita. Da yawa daga cikin wadanda cutar ta kama da ma wadanda suka mutu sakamakon kwayar cutar ta Ebola dai, na cikin kauyuka inda aka samu rahoton bullar cutar guda 20 a Beni.