1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar kwalara ta halaka gomman rayuka a arewacin Najeriya

September 19, 2025

An sake samun bullar cutar kwalara a jihar Bauchi a Najeriya, inda ta yi sanadin gomman rayuka da ma kwantar da wasu daruruwa. Hukumomin jihar sun ce tuni aka fara daukar matakan dakile ta.

Wasu kananan yara 'yan karkara a yayinn neman ruwa a Najeriya
Wasu kananan yara 'yan karkara a yayinn neman ruwa a NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/Gilbertson

Rahotannin da ke fitowa daga Najeriya, na cewa cutar kwalara ta kashe mutane 58 tare da kama wasu sama da 250 a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin kasar.

Hukumomi da suka tabbatar da labarin a ranar Juma'a, sun ce lamarin da ya sanya kafa sabbin kwamitoci domin karfafa martani na gaggawa da kuma hanyoyin rigakafi.

Cutar ta kwalara, wacce ke yaduwa ta hanyar abinci da ruwa da suka gurbace, ba sabon aba ba ce a Najeriya inda jami'an lafiya ke danganta ta da karancin ruwan sha mai tsafta a yankunan karkara da kuma cikin lungunan birane.

A cewar cibiyar yaki da cututtuka da rigakafi ta Najeriya NCDC, ta samu fiye da labarin kamuwar mutum akalla dubu 11 tare da mace-mace sama da 400 cikin shekaru biyu da suka gabata, inda yara kasa da shekaru biyar suka fi kamuwa da cutar.