1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Cutar kwalara ta kashe sama da mutane 500 a Zambiya

Zainab Mohammed Abubakar
January 24, 2024

Zambiya ta dage zangon karatun wannan shekarar a karo na biyu, sakamakon barkewar cutar kwalara da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 500.

Hoto: Shiraaz Mohamed/AFP

Tun a ranar 8 ga watan Janairu ne ya kamata a bude makarantu a kasar ta kudancin Afirka, amma a makon jiya gwamnati ta mayar da ranar zuwa 29 ga watan Janairu.

A wannan Larabar ce dai, ta ba da sanarwar karin jinkiri, bisa la'akari da ta'azzarar cutar. Ministan ilimi Douglas Syakalima ya shaida wa manema labarai a Lusaka babban birnin kasar, inda cutar ta bulla, an umurci ma'aikatar ilimi ta kara dage ranar bude makarantun zuwa 12 ga Fabrairu.     

Kasar Zambiya dai na fama da yaduwar kwalara tun a watan Oktoba, cutar da ke da nasaba da amfani da gurbataccen ruwa ko abinci. Cikin sao'i 24 da suka gabata, an samu sabbin kamuwa kimanin 438 kana wasu mutane shida sun mutu, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 518, in ji ministar lafiya Sylvia Masebo.

A makon da ya gabata, zambiyar ta samu rukunin farko na farko na alluran rigakafin cutar ta kwalara fiye da miliyan guda daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) don yaki da barkewar cutar. Masebo ta ce mutane miliyan 1.4 ne suka samu rigakafin.