1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Cutar kyandar biri ta bulla a karon farko a Ghana

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim MAB
October 4, 2024

Daga watan Janairu zuwa yanzu, fiye da mutane 860 cutar ta kyandar biri ta halaka a nahiyar Afirka ciki har da Ghana, bayan da ta kama mutane 34,297, in ji hukumar CDC mai yaki da yaduwar cututtuka ta Afirka.

Yara sun fi kamuwa da cutar kyandar biri a kasashen Afirka
Yara sun fi kamuwa da cutar kyandar biri a kasashen AfirkaHoto: Ruth Alonga/DW

Ghana ta tabbatar da bullar cutar kyandar biri a karon farko a kasar, bayan da ta kama wani yaro a yankin Yamma maso arewacin kasar, a daidai lokacin da take ci gaba da yaduwa a nahiyar Afirka. Babban daraktan hukumar lafiya ta kasar Patrick Kuma-Aboagye, ya ce tuni suka killace yaron bayan da nuna alamun kamuwa da cutar, wato zazzabi da ciwon gabobobi, inda suke gudanar da bincike a kan mutane 25 da suka kusance shi, don tabbatar da sanin ya ya koshin lafiyarsu yake.

 

Karin bayani:Kwango na maraba da tallafin rigakafin Mpox

Babban jami'in na Ghana ya kara da cewa akwai rahotannin mutane 230 da suke gudanar da gwaje-gwaje a kansu, don kauce wa yaduwar cutar mai saurin kisa.Daga watan Janairu zuwa yanzu, fiye da mutane 860 cutar ta kyandar biri ta halaka a nahiyar Afirka, bayan da ta kama mutane 34,297, kamar yadda shugaban hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Afirka CDC Jean Kaseya ya sanar jiya Alhamis.