1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaAfirka

Cutar kyandar biri ta mpox ta halaka mutane a Kamaru

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim MAB
September 12, 2024

Cutar ta fi kamari a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Burundi da Kwango-Brazzaville da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, amma ta bulla kasar Kamaru inda ta kashe mutane biyu.

Hoto: Ruth Alonga/DW

Hukumomi a kasar Kamaru sun tabbatar da mutuwar mutane 2 da suka kamu da cutar kyandar biri ta Mpox, tare da ci gaba da nazartar lafiyar wasu mutane 40 da ake zargin sun kamu da cutar, tun bayan barkewar annobar a watan Afirilun da ya gabata.

Karin bayani:Kwango na maraba da tallafin rigakafin Mpox

Ministan lafiyar kasar Malachie Manaouda, ya ce daga cikin mutane 46 da aka yi wa gwaji, an gano 6 daga cikinsu na dauke da cutar kyandar biri, kuma tuni suka yi nisa wajen gudanar da rigakafinta a fadin kasar, tare da fadakar da jama'a kan hanyoyin kare kai daga kamuwa da ita.

Karin bayani:Jamus na taimaka wa Kwango gano masu fama da kyandar biri

Ya zuwa yanzu dai, an gano bullar cutar a kasashe 14 na Afirka, kuma ta fi kamari ne a kasashen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Burundi da Kwango-Brazzaville da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kamar yadda hukumar dakile yadurar cututtuka ta Afirka CDC ta tabbatar.