1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar maleriya na addabar 'yan Yuganda

April 4, 2017

Yaki da cutar zazzabin cizon sauro na fuskantar kalubale a Yuganda sakamakon talauci da 'yunwa da al'ummar kasar ke fuskanta, a daidai lokacin da ake shirin raya ranar yaki da Maleriya ta duniya a 25 ga watan Afirilu.

Malaria Mücke
Hoto: picture alliance/blickwinkel/Hecker/Sauer

Joselyn Nahabwe, yarinya ce 'yar shekara uku da ke fama da cutar tamowa da zazzabin cizon sauro. Saboda haka ne mahaifiyarta ta zauna a kofar asibitin Namusitu da ke gundumar Budaka a yankin gabashin Yuganda har na tsawon awa 6, ta na jiran a ba wa yarta maganin maleriya. Idan ba su samu magani a kan lokaci ba, yarinyar na iya mutuwa, kamar dubban wadanda ke rasa rayukansu a kowace shekara sakamakon cutar.


Amma idan Joselyn ta tsira daga zazzabin cizon sauro, to mahaifiyarta zata samu gidan sauro mai dauke da magani wajen kare 'yar ta daga kamuwa da cutar a gaba. Sai dai kuma jama'a da dama na cewa 'yunwa ce ke addabar su, don haka gidan sauron ba shi da wani muhimmanci a garesu. Sakamakon wani dadadden fari, jama'a  ba su da abin da za su ci, wadda hakan kuma ya sanadiyar mutuwar mutane da yawa musamman ma a yankunan Gabas da Arewa maso gabashin Yuganda. 

Tuni ma'aikatar lafiya ta fara kokarin fadakar da al'umma kan dalilan da yasa ya zama dole su yi amfani da gidan sauron maimakon  bayar da shi domin karbar abinci. Vivian Serwanja mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar ta Yuganda, ta ce "Muna so mu ga ana amfani da gidan sauron, saboda  jama'a sun rage zuwa wajen likita saboda zazzabin maleriyar, kun san cewa jinyar ta yafi rigakafin ta tsada." 

Gwamnatin Yuganda na raba gidajen sauro da ke dauke da magani kyautaHoto: Ralph Ahrens

 

Kwararru a harkar lafiya sun yi imanin cewa talauci da 'yunwa za su iya kawo koma baya a kokarin da ake na yakar zazzabin cizon sauro, matukar ba a bullo da wani shirin raba wa jama'a abinci ba. Hakan ne ma ya sa Ministar lafiya ta kasar take rokon jama'a da su tsabtace gidan sauron, sannan su dinke duk wani huji da ya samu lokacin amfani da shi."

Wata kididdiga daga ma'aikatar lafiya ta Yugandan ta bayyanna cewa cutar maleriya ce ke kan gaba wajen kashe mutane fiye da kowace cuta a kasar. Yuganda ce me kasa ta 6 a jerin kasashen da maleriya tafi kashe jama'a a nahiyar Afirka baki daya.