1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Cutar Marburg mai kama da Ebola ta halaka mutane a Rwanda

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
October 1, 2024

Ana samun cutar Marburg daga jikin jemage, wadda ke haddasa matsanancin zazzabi da fitar jini bayan gurbatarsa, sannan tana saurin halaka mutum da zarar ya kamu da ita.

Hoto: Merlin D. Tuttle, Bat Conservation International, www.batcon.org.

Rwanda ta sanar da mutuwar mutane 8 a kasar, sakamakon kamuwa da cutar Marburg mai kama da Ebola, kwanaki kalilan bayan ayyana barkewar cutar da ba ta da magani ko rigakafi a hukumance.

Ana samun cutar Marburg daga jikin jemage, wadda ke haddasa matsanancin zazzabi da fitar jini bayan gurbatarsa, sannan tana saurin halaka mutum da zarar ya kamu da ita.

Karin bayani:Bullar cutar Marburg a Equatorial Guinea

Ya zuwa yanzu dai mutane 26 ne suka kamu da cutar a Rwanda, 8 daga cikinsu kuma suka mutu, bayan barkewarta a ranar Juma'ar da ta gabata.

Karin bayani:WHO: Marburg ta sake bazuwa a Ghana

Ministan lafiyar kasar Sabin Nsanzimana, ya ce sun killace mutane 300 da ake kyautata zaton sun yi mu'amala da wadanda su ka kamu da cutar, domin duba lafiyarsu, da kuma dakile yaduwarta a kasar.