Cutar murar tsuntsaye ta kara bulla a kasar Sin
November 29, 2005Talla
Rahotanni daga kasar Sin sun nunar da kara bullar cutar murar tsuntsaye a kasar. Wannan bayanin dai ya fito ne daga bakin maikatar kula da aiyukan noma ta kasar.
Bisa kuwa hakan tuni jami´an gwamnatin kasar suka bayar da umarnin halaka dubbannin tsuntsaye dake wani gidan gona a arewa maso yammacin yankin Xinjiang.
Daga dai tun lokacin da wannan cuta ta bulla a kasar ta sin ya zuwa yanzu, bayanai sun shaidar da cewa tsuntsaye a kalla miliyan ashirin aka halaka a kasar a kokarin da ake na dakile yaduwar cutar izuwa wasu gurare na daban.