Polio ta sake kunno kai a kasar Sudan
September 2, 2020Talla
A wani abin da ke zaman ta leko ta koma a nahiyar Afrika, mako guda bayan da Hukumar Lafiya ta Majalissar Dinkin Duniya WHO ta ayyana nahiyar a matsayin wadda ta shawo kan cutar Polio, a karon farko bayan wannan ikirarin an samu bullar cutar a Sudan.
An dai samu wasu yara guda biyu dauke da cutar shan Inna wadda ta kanannandesu tun a watan Maris da Afirilu gabanin a tabbatar da cewa shan Inna ce. Yaro na farko da aka samu ya fito ne daga yankin Darfur yayin da gudan kuma ya fito daga yankin Gedarif da ke makwabtaka da kasashen Habasha da Eritriya.
Hukumar lafiyar ta WHO ta ce yanzu haka akwai wasu da dama da ake hasashen cutar ta Polio ce ta kamau su, amma ya zuwa yanzu babu tabbacin hakan.