1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka ta Kudu

Afirka ta Kudu: Majalisar dokoki za ta zabi shugaban kasa

Abdourahamane Hassane
June 14, 2024

Nan gaba a yau sabbin ‘yan majalisar dokoki 400 da aka zaba a karshen watan jiya a Afirka ta Kudu, za su kada kuri'a domin zaben shugaban kasa da mataimakinsa da kakakin majalisar dokokin.

Hoto: Solomon Muche/DW

 Shugaba Cyril Ramaphosa wanda jam'iyyarsa ta ANC ta rasa rinjaye a karon farko cikin shekaru 30, wadda ke da  kujeru 159 na kokarin kula kawance da jam'iyyun siyasa na adawa.Yaynzu haka dai akwai labaran da ake bayyanawa cewar ANC za ta  yi kawance da Democratic Alliance (DA) mai kujeru 87 da kuma Inkatha Freedom Party (IFP) mai kujeru 17 domin samun rinjaye kujeru 250 don kafa   gwamnati.