Taliban ta aika jami'anta zuwa kasar Jamus
August 29, 2026
Talla
Gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta aike da wata tawagar jami'an diflomasiyya zuwa Jamus, kamar yadda gidan rediyon NDR na kasar ya ruwaito.
Jami'an uku za su shafe makonni uku a Jamus, kuma a halin yanzu suna ofishin jakadancin Afghanistan da ke Berlin.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Jamus ta tabbatar da kasancewar tawagar, tana mai cewa ziyarar na da nasaba da shirye-shiryen sake mayar da wasu 'yan kasar Afghanistan daga Jamus zuwa kasarsu.
Shekaru biyar bayan Taliban ta sake karbar iko a Kabul, har yanzu Rasha ce kadai ta amince da gwamnatinta a hukumance.