Da alama Koriya Ta Arewa na shirin gudanar da sabon gwajin makamin nukiliya
October 28, 2006Talla
Jami´an sojin KTK sun ce sun ga wani kai-komo a wurin da ake zargin cewa KTA ta gudanar da gwajin makamin nukiliya, wanda hakan ke nuni da cewa kasar mai bin tsarin kwaminisanci na shirye shiryen yin sabon gwaji. Kamfanin dillancin labarun KTK Yonhap ya rawaito majiyoyin soji wadanda suka ce suna sa ido akan zirga-zirgar manyan motoci da kai-komon sojojin KTA a wannan wuri dake can yankin karkara na arewa maso gabashin kasar ta KTA. A ranar 9 ga watannan na oktoba KTA ta yi gwajin makamin nukiliyan ta na farko wanda janyo sanyawa gwamnati a birnin Pyongyang takunkumin kwamitin sulhun MDD.