1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An kama hanyar kafa gwamnati a Jamus

October 16, 2021

Jam'iyyun da ake zawarcinsu a Jamus, sun ce akwai alamun samun fahimtar da za ta kai ga kafa gwamnatin da za ta gaji Angela Merkel, a ci gaba da tattaunawa da suke yi.

Pressekonferenz nach Ampel-Sondierungsgesprächen
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Ga dukkan alamu dan takarar jam'iyyar SPD a nan Jamus, Olaf Scholz, na kan hanyar jagorantar gwamnati, bayan sanarwar soma cimma yarjejeniya da jam'iyyarsa ta yi da jam'iyyun the Greens ta masu kare muhalli da kuma FPD, masu ra'ayin ci-gaban kasuwanci.

Jam'iyyun uku dai na ta tattaunawa ne dai tun bayan 'yar galaba da Olaf Scholz din ya samu a zaben ranar 26 ga watan Satumban 2021, zaben da dan takarar jam'iyyar CDU ta Angela Merkel, wato Armin Laschet ya zo na biyu.

'Yar takarar jam'iyyar the Greens, Annalena Baerbock, ta ce ganawar da suka yi dai ta nuna manyan alamu na kafa sabuwar gwamnatin da za ta maye ta jam'iyyar CDU ta masu ra'ayin mazan jiya.

Sai dai shi ma Armin Laschet, na jam'iyyar CDU na cewa akwai fatan kafa gwamnatin.