1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Da alamun kallo a zaben jihar Ekiti ta Najeriya

July 12, 2018

Yayin da ake gab da zaben gwamna a jihar Ekiti da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya, hankali na kara tashi sakamakon zargin barazana da take hakki da PDP ke yi kan jami'an 'yan sanda.

Wahl in Nigeria
Hoto: Reuters/Afolabi Sotunde

Yayin da ake gab da zaben gwamna a jihar Ekiti da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya, hankali na kara tashi a jihar sakamakon zargin da gwamna mai ci Ayodele Fayose ya yi na cewar rundunar ‘yan sanda na neman halaka shi.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai wasu jami’an ‘yan sanda suka yi harbe-harbe tare da watsa borkonon tsohuwa lokacin gangamin yakin neman zabe na jam’iyyar PDP, lamarin da ya sanya gwamnan kokawa da hawaye tare da dora alhakin abin da ya faru ko ma zai faru nan gaba a kan sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriyar.

Tun da fari dai sai da jam’iyyar PDPn ta yi zargin cewa ba za a yi mata adalci ba a zaben, wanda a shirye-shiryensa aka baza dubban jami’an ‘yan sanda.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, tana ci gaba da aikinta na rabbara kayan zabe, tare kuma da amincewa da yawan jami’an tsaron saboda kare kayan aiki da ma ma’aikatan da za su gudanar da zaben na ranar Asabar da ke tafe.

Wasu dai na cewa gwamnan na Ekiti bai sami yanda yake so ba ne ya sa shi wannan ikirari. Hasali ma kaikayi ne ya koma kann mashekiya, saboda ganin iirin abin da ya aikata a zaben baya na yin amfani da karfi kann masu adawa a jihar.