Halitta da Muhalli
Daftarin taron Masar
November 17, 2022Talla
An fara rubuta daftarin taron kare muhalli na COP27 da ke wakana a kasar Masar kan sauyin yanayi inda ake fatan ganin dumamar duniya bai fi maki 1.5 a ma'aunin zafi, amma akwai wasu wurare da ake ganin za a iya samun sabani tsakanin kasashen duniya.
A wannan Jumma'a ake kawo karshen taron mai yuwuwa ba tare da samun duk kasashen sun amince da matsayi guda ba. Akwai yuwuwar samun kalamai ba masu sassauci, musamman kan ci gaba da amfani da man fetur maimakon makamashin da ake sabuntawa. Sai dai tun farkon wannan makon kasashen Amirka da China da suke kan gaba wajen karfin tattalin arziki a duniya kuma na gaba wajen fitar da iskar da ke gurbata muhalli sun amince da aiki tare.