1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daga ina Falasdinawan Gaza ke samun makamansu?

July 11, 2014

A daidai lokacin da ake ci gaba da dauki ba dadi tsakanin Falasdinawa da Isra'ila, ana ci gaba da dasa ayar tambaya kan yadda Falasdinawan ke samun makaman da ke barazana ga tsaron Isra'ilan.

Hoto: Said Khatib/AFP/Getty Images

A daidai lokacin da kungiyoyin Falasdinawan Gaza masu gwagwarmaya ke mai da martini kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa yankinsu, ta hanyar harba rokoki kan garuruwan Isra'ilan, ana ci gaba da dasa ayar tambaya kan yadda kungiyoyin ke samun wadannan makamai.

Duk da takunkumin da aka yi shekaru ana garkama wa yankin na Gaza, ta hanyar killaceshi da Isra'ila ta yi ta bangaranta da rurrusa hanyoyin fasa kwauri ta karkashin kasa da Masar ta yi a yankin Rafah da ita kasar ta Masar ke ci gaba da killaceshi, in banda wasu 'yan lokutan da take budeshi don zirga-zirgar marasa lafiya da mahajjata, gami da hana shigar wa yankin kayayyakin gine-gine da sinadiran da za a iya amfani da su wajen kera makamai, duk da wadannan tsauraran matakai, kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza, wato Hamas da Jihadul Islami, na ci gaba da samun rokokin da suke kada hantar bani Yahudu da su.

Ibrahim Abu Sa'ada, kwararre kan dabarun yaki da sarrafa makamai, yayi nuni da cewa, ginshikin makamai da rokokin da Falasdinawan ke harbawa kan Isra'ila, shi ne kirar gargajiyar da aka bunkasata ta hanyar fasahar zamani:

"Wadannan rokoki da muke kira Yaseen, mu da kanmu muke kerasu, kuma muke ci gaba da bunkasasu. Wadannan rokoki za su iya isa garuruwan Haifa da Tel Aviv da birnin Qudus. Harbasu da muke, koda yake wani lokacin ba sa samun yadda aka kwatasu, amma duk da hakan suna birkita Yahudawa da kuma dama musu lissafi."

Kasar Iran, da ke zama babbar abokiya ta kut da kut ga al'ummar Falasdinawa, duk da tsangwamar da take fuskanta daga kasa da kasa, ita ce kashin baya wajen tura wa kungiyoyin Falasdinawan masu gwagwarmaya makamanta da ta kera, ko makamai kirar Rasha da Koriya ta Aarewa daga kasuwannin bayan fage tana tura wa Falasdinawan. Kuma a baya bayanan, ta tura musu rokoki samfaren Fajr masu cin dogon zango. Ramadan Shalha, shi ne shugaban Baraden Jama'atul Islamiyya:

"Dangane da gwagwarmayar da mu Falasdinawa ke yi kan mamayar Isra'ila, kasar Iran na goyan bayanmu dari bisa dari, kuma yawancin makaman da muke amfani da su wajen kare kanmu daga cin zalin sojojin Sahayina, daga kasar Iran muke samunsu. Ko dai ta hanyar bamu makamanta da ta kera ko kuma ta hanyar sayo mana makaman."

Wata hanyar da Falasdianwan ke samun makaman nasu ita ce hanyar fasa kwaurin makaman da ake sayowa daga kasar Libiya ana shigowa da su ta hanyoyin karkashin kasa. Duk da rusa yawancin hanyoyin da sabuwar gwamnatin sojan Masar ta yi, Falalsdinawan na ci gaba da bin hanyoyinsu da su suka sansu, wajen fasa kwaurin makaman. Yazil Yusuf, jami'i ne a ma'aikatar tsaron Masar:

Pirayim Ministan Israila Netanyahu(tsakiya) da kwamandojinsaHoto: picture-alliance/dpa

"Mun samu bayanan asirai da ke nuni da fasa kwaurin makaman da ke kakkabo jiragen yaki, daga rundunar sojin Libiya zuwa zirin Gaza. Kadan Masar ba ta dauki matakan hana irin wannan ba, yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kulla da Isra'ila kan iya rugurgujewa. Don haka dole ne a ci gaba da hana shigar da makamai ta cikin Masar zuwa Gaza."

Kamar dai yadda kwarraru ke kara tabbatarwa, rikice-rikicen yankin na Gabas ta Tsakiya, da kara tabarbarewar lamarin tsaro, da karancin sa ido a iyakoki, batu ne da zai ba da damar hada-hadar makamai a kusan ko ina a yankin, musamman zuwa yankin na Gaza da al'umomin Larabawa ke jin cewa an mayar da su 'ya'yan bora.

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Umaru Aliyu