1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dage dokar ta baci a Siriya

Halimatu AbbasApril 21, 2011

Shugaban Siriya, Bashar Al-Assad ya da umarnin dage dokar ta-baci da a kakaba tun shekaru 50 da suka gabata.

Shugaba Assad a lokacin da yake jawabi ta telebijanHoto: dapd

Gidan telebijan kasar Siriya ya ba da rahoton da ke nuni da cewa Shugaba Bashar Al-Assad ya ba da umarnin dakatar da dokar ta-baci da aka gindaya kusan shekaru hamsin da suka gabata-matakin da za rusa kotuna na musamman ya kuma ba al'uma damar gudanar da zanga-zanga a cikin limana. Akalla mutane 21 suka rasa rayukansu a wannan mako bayan da aka gudanar da zanga-zangar samar da walwalar siyasa da kuma yin kira ga shugaba Assad da ya yi murabus. A dai halin da ake ciki yanzu an baza dakarun sintiri masu saye da rigunan farar hula dauke da bindigogin AK 47 domin kamen 'yan zanga zanga.

Mawallafiya Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal