Dage shari'ar mahukuntan Kenya
September 11, 2013An dage sauraron karar mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto tare da wani dan jaridar kasar Joshua Arab Sang, a Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa "ICC" dake da shalkwata a birnin "The Heague" na kasar Holland.
Kotun ta ICC dai na tuhumar mataimakin shugaban kasar ta Kenya Mr. William Ruto da kuma dan jarida Joshua Arab Sang, da aikata laifukan yaki a yayin rikicin bayan babban zabe da aka yi a kasar ta Kenya a shekara ta 2007, da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyin al'umma da dama.
Da yake bayyana dalilan da suka sanya aka dage sauraron karar, Alkalin kotun mai shari'a Eboe Osuji yace, an dage sauraron shari'ar ne zuwa ranar Talata mai zuwa wato 17 ga wannan wata na Satumba da muke ciki, bisa dalilan rashin zuwan shaidu a kan lokaci kamar yadda kotun ta bukata.
Alkalai sun bayyana dage shari'ar Mr. Ruto
Sai dai kuma ko ya ya mataimakin shugaban kasar ta Kenya William Ruto ya dauki wannan dage karar da aka yi? Wata 'yar jarida daga kasar ta Kenya Zubaida Kananu da ta halarci harabar kotun ta bayyana cewa wadanda ake karar basu ji dadin dage sauraron shari'ar da kotun ta yi ba.
Ta ce " Bai ji dadi ba, shi ma lauyan dake kare wadanda ake tuhuma Kareem Khan ya nuna rashin jin dadinsa bayan da aka dage karar sai dai ya ce za su dawo ranar Litinin mai zuwadomin halartar zaman kotun a ranara Talata. Lokacin da aka fara sauraron karar kowa ya tsammaci za a kammala sauraron shari'ar cikin sauki"
A cewar wani Lauya Gordian Mwikira alkalai na da ikon dage karar bisa dalilai da dama, sai dai kuma lauyoyin wadanda ake kara ka iya kalubalantar dage shari'ar in har suna da wani kwakkwaran dalili.
Ya ce "In har masu kare wadanda ake kara suka ga babu wani kwakkwaran dalili na dage kara, suna da damar kalubalantar kotu, sai dai ya rage ga alkalan dake sauraron shari'ar su amince da bukatarsu ko kuma su ki amincewa".
A kwai dalilai da dama dai da ake ganin sun sanya fuskantar matsaloli dangane da sauraron wanan kara da ke da tarihi a kotun ta ICC, inda da dama ke ganin matsalar da ake fuskanta ta rashin halartar shaidu, bata rasa nasaba da cewa wadanda kotun ke tuhuma suke rike da ragamara mulki a kasar ta Kenya kamar yadda Zubaida Kananu ta bayyana.
Fargabar ci gaba da samun rashin shaidu a shari'ar
Ta ce " Wannan ne karo na farko da kotun ke tuhumar shugaban kasa mai ci tare da mataimakinsa. Abu ne mai matukar wahala ace wani zai tsaya a gaban kotu ya bada shaida a kan shugaban kasarsa. Mutane da dama na ganin cewa gurfanar da shugaban kasa a gaban kotu da kuma kawo mutane daga kasarsa domin su bada shaida a kan abin da ake tuhumarsa da shi, shine babban kalubalen da kotun za ta fuskanta. Sannan mutane na ganin cewa wannan shine babban dalilin da ya sanya shaidu da dama suka yanke shawarar janyewa, koda shaidu uku na farko dake kare masu kara sun yanke shawarar janyewa daga bada shaidar".
A ranar 10 ga wannan wata da muke ciki ne dai, kotun ta fara sauraron tuhumar da ake yiwa mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto da kuma dan jarida Joshua Arab sang, ta hanyar karanta musu laifukan da ake zarginsu da aikatawa, zargin da dukkaninsu ke ci gaba da musantawa.
Mawallafiya:Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasir Awal