Lamura na kara dagulewa a Gabas ta Tsakiya
March 2, 2026
Sojojin Isra'ila sun yi gargadin kara tsananta hare‑haren da suke kai wa a Lebanon kan mayakan kungiyar Hezbollah mai goyon bayan Iran, a wani mataki na rama wa kura anniyarta bayan da kungiyar ta shiga yakin Iran gadan-gadan. Da yake magana da manema labarai a dazu Janar Rafi Milo babban kwamandan rundunar Isra'ila ya ce hare-haren za su tsananta, kuma Isra'ila ba za ta daga kafa ba har sai ta cimma burinta a yankin, yana mai bayyana cewar Hezbollah, za ta dandana kudarta.
Tashin hankali na kara yin muni a Gabas ta Tsakiyya
Wannan lamarin na zuwa a yayin da a gefe guda, kungiyar Kataeb Hezbollah mai goyon bayan Iran a Iraki, ta sanar a wannan Litinin da yi wa wani sansanin sojanta mafi girma na Jurf al‑Nasr luguden wuta. Isra'ila ta sanar da cewar za ta ci gaba da kai hare-harenta a Iran face sai ta kakkabe abin da ta kira 'yan ta'adda, a yayin da kafar yada labaran Iran ta sanar da jin karar ababen fashewa a Teheran.
Amurka da Isra'ila sun kai wa Iran hari
An ji fashewar bama-bamai a Dubai da Bahrain inda mutun guda ya kwanta dama. a yayin da Amurka ta sanar da mutuwar sojojinta uku, lamarin da shugaban Donald Trump ya sanar da cewar ba zai taba bari Iran ta sha ba, tare da kira ga sojan Iran da su mika wuya ko su bankwaci lahira. Inda ya ce "Iran na ci gaba da harba makamai nukiliya masu cin dogon zango, kana makaman nukilyarsu za si iya zama bazana ga kowane dan Amurka".
Fadar White House za ta yi bayani kan matakin Amurka a gaban majalisa
A wannan Litinin shugaba Donald Trump zai ta fara yi wa majalisar dokoki bayani game da matakin sojin da Amurka ta dauka akan Iran, a daidai wannan lokaci da ra’ayoyin ‘yan kasa suka bam-bamta. Kafofin samun labarai daga White House sun ce a wannan Litinin, mukarraban gwamnatin Trump da suka da sakataren Tsaro Pete Hegseth da takwaran aikinsa na harkokin waje Marco Rubio, za su gana da shugabannin kwamitin aikin soji da na harkokin waje a majalisar dattawa da ta dokoki game da wannan yaki da ra’ayoyin Amurikawa suka bambamta akan dacewa da rashin dacewarsa.
Iran ci gaba da mayar da martani da makamai masu linzami
An ji karar fashe‑fashe da dama da sanyin wannan safiya a Jérusalem inda karaurawar kartakwana ta garkuwar sararin samaniyar Isra'ila dinga amo, sakamakon harba makamai masu linzami zuwa Isra’ila da Iran ta yi, kazalika an ji karara wasu ababen fashewa a birnin Tel Aviv, da ke tsakiyar kasar Isra'ila, a yayin da rundunar tsaron Isra'ilar dai ta ci gaba da gargadin 'yan kasar da su kasance a mabuyar karkashin kasa a wani mataki na kare kai daga hare-haren makamai masu linzamin da Iran ke harbawa, a yayin da bangarorin biyu ke ba ta kashi.