Dakarun Burkina Faso sun kashe 'yan ta'adda
September 3, 2023Talla
A sanarwar da sojojin suka fitar da yammacin jiya sun ce, lamarin ya auku ne a ranar Juma'ar da ta gabata, kuma sun yi nasarar lalata motoci da mashinan 'yan ta'addar gami da kwace manyan makamai da magunguna, su kuma a nasu bangaren sun yi asarar jami'ansu 5.
Kasar Burkina Faso da ke yammacin Afirka ta jima tana fama da ayyukan wadannan mayakan da ke da alaka da kungiyoyin al-Qaeda da IS.
A baya shugaban gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traoré ya tabbatar da karfin 'yan ta'adda da ke haddasa tashin hankali a kasar ya karu matuka.
Sama da mutum miliyan biyu ne rikicin 'yan ta'addar kasar Burkina Faso ya raba da matsugunansu yayin da dama suka rasa rayukansu.