1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun gwamnati a Jamhuriya Afrika ta tsakiya sun ƙwato filin jirgin Birao

March 6, 2007

Dakaru masu biyaya ga gwanatin Jamhuriya Afrika ta tsakiya, sun ƙwato filin saukar jiragen sama, na birnin Birao a yankin arewa maso gabacin ƙasar daga hannun yan tawaye.

Hamad Hamadeen kakakin ƙungiyar tawayen, ya tabbatar da wannan labari , to saidai kuma ya nunar da cewa janyewar su daga wurin, wani mataki ne, na ja da baya ba tsoro ba.

Rundunar tawayen Jamhuriya Afrika ta tsakiya, ta zargi sojojin France, ta tallafawa dakarun gwamnati.

Sanarwar daga fadar mulki a birnin Pari,s ta mussanta wannan zargi, saidai ta ce jirgin yaƙin France, ya maida martani ga rundunar yan tawaye, a sakamkon harin da su ka kai, ga sojojin sa iddo na France