1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun gwamnatin Libiya sun karɓe iko da tashar jiragen ruwan Sirte

Bowen, AndrewSeptember 27, 2011

Sojojin gwamnatin wucin gadin Libiya sun ce sun fara yin galaba a birnin Sirte mahaifar Gaddafi, inda har yanzu Kanar Gaddafi ke da magoya baya

Wani maƙin a Sirte daga cikin sojin gwamnatin wucin gadin LibiyaHoto: AP Photo/Xinhua

Sabuwar gwamnatin Libiya ta fara galaba a birnin Sirte, mahaifar tsohon shugaba Muammar Gaddafi. Sojojin gwamnatin wucin gadin sun karbi jagorancin wata tashar jiragen ruwa bayan da suka kutsa cikin birnin. Daruruwan fararen hula sun kaurace daga Sirte sakamakon barazanar rincabewar rikici. Sirte na daya daga cikin wuraren da basu riga sun kasasnce a karkashin jagorancin sabuwar gwamnatin kasar ba. To sai dai daya daga cikin kwamandojin rundunar sojin kasar ya ce yana tattaunawa da wani dattijo daga kabilar Gaddafin domin cimma wata yarjejeniya. ko da shi ke a can a Bani Walid inda nan ma Kanar Gaddafi ke da magoya baya ana cigaba da dauki ba dadi.

A wani labarin kuma, Wata kotun daukaka kara a Tunisiya ta sako tsohon Frime Ministan Kanar Gaddafi Al-Baghdadi Ali al-Mahmoudi wanda aka yanke masa hukuncin watanni shidda a gidan kaso bayan da aka cafke shi kusa da Iyakar kasar da Aljeriya a makon da ya gabata. Lauyar sa Mubarak Korchid ya fadawa kamfanin dillancin Reuters cewa mai shari'ar ya sako Mahmoudi da ma'aikatansa guda biyu bayan da aka zarge sa da shiga kasar ta haramtacciyar hanya.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita : Usman Shehu Usman