1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun gwamnatin Siriya sun kashe 'yan zanga-zanga

August 5, 2011

Gwamnatin Siriya na ci gaba da ɗaukar matakin ba sani ba sabo akan masu boren nuna adawa da ita

Tankokin soja a garin HamaHoto: AP Photo / SHAMSNN

A kusa da birnin Damaskun na ƙasar Siriya an samu mutuwar 'yan zanga-zanga da dama bayan da dakarun tsaro suka buɗe musu wuta tare kuma da yin amfani da gas mai sa hawaye domin tarwatsa su . Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hilary Clinton ta yi kira ga ƙasashe da dama da su yi wa Siriya matsin lamba a baya ga yin Allah wadai da wannan rikici. 'Yan rajin kare haƙƙin bil Adama sun ce sai da ma dakarun gwamnati suka kashe wasu 'yan zanga zanga hudu bayan sallar ashan jiya da daddare. A shekaran jiya Laraba komitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya yi Allah wadai da matakan take bil Adama da gwamnatin Siriya ke ɗauka akan al'umarta. Mutane ɗari ne dai suka rasa rayukansu a wannan mako a garin Hama a cikin arangamar da aka yi tsakanin yan zanga-zanga da soji.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal