1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun gwamnatin Sudan sun mamaye Abyei

May 22, 2011

An kama hanyar faɗawa saban rikici tsakanin yankunan kudu da na arewacin Sudan, bayan da dakarun gwamnati su ka mamaye Abyei

Hoto: AP

Gwamnatin kudancin Sudan ta zargi hukumomin Khartum da mamaye yankin Abyei.

Tun dai jiya Asabar ne dakarun gwamnatin Sudan suka mamaye Abyei da sauran lardunan da ke kewaye da ita.Wannan mamaya ta faru a yayin da ya rage wata guda kacal yankin kudu ya ƙadammar da bikin ɓallewa daga ƙasar Sudan.

Sadiq Amer mai maganin da yawun gwamnatin Khartum ya bayyana dalilan ɗaukar wannan mataki da cewa Abyei yanki ne mallakar arewacin Sudan, saboda haka ya zama wajibi su fidda duk sojojin yankin Kudumm, wanda a cewar sa Kasancewar su Abiye ya saɓawa yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattabawa hannu a shekara 2005.

Ƙasashen yammacin duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya, sun yi Allah wadai da wannan mamaya, wadda su ka ce za ta maida hannun agogo baya, game da zaman lafiyar da aka cimma tsakanain yankunan kudu da na arewacin Sudan bayan fiye da shekaru 20 na tattanawa.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Zainab Mohamed Abubakar