Indiya da Faransa na atisayen sojoji
January 25, 2019Talla
A shekarar bara ne dai Faransa da Indiya suka cimma wata yarjejeniya ta karfafa huldar tsaro a tsakaninsu. Kaso 25 cikin 100 na sufurin jiragen ruwa na duniya na bi ta tekun na Indiya, yayin da kasashen Turai ke da kaso 75 na yawan jiragen ruwan da ke ratsa tekun. Indiya wacce ke yin zaman doya da man ja tsakaninta da China sakamakon yadda take kara mamaye tekun Indiyar, na kallon atisayen a matsayin kandagarki.