Dakarun kawance sun kaddamar da sabon farmaki a Afghanistan
September 16, 2006Talla
Dubun dubatan dakarun kawance dake karkashin jagorancin Amirka da sojojin Afghanistan sun kaddamar da wani sabon farmaki kan ´yan Taliban a wasu larduna biyar na Afghanistan. Wannan farmakin ya zo ne a daidai lokacin da dakarun da kungiyar tsaro ta NATO kewa jagoranci ciki har da sojojin Amirka dubu 2 da 500 ke ci gaba da fafatawa da ´yan Taliban a kudancin Afghanistan. Kawo yanzu an halaka daruruwan ´yan Taliban a cikin makoni 2 da fara wannan farmaki. A wani ci-gaban kuma Canada ta kara yawan dakarunta a Afghanistan da sojoji 200.