1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Mali sun kwace Kidal

Suleiman Babayo USU
November 15, 2023

Dakarun Mali sun bayyana samun nasarar sake kwace garin Kidal na arewacin kasar mai tasiri daga hannun 'yan tawaye.

Sojojin da ke mulkin Mali
Sojojin da ke mulkin MaliHoto: AP Photo/picture alliance

Sojojin Mali sun sake kwato garin Kidal na arewacin kasar mai tasiri daga hannun mayakan 'yan tawayen aware na Azbinawa, wadanda suke ci gaba da zama kadangaren bakin tulu ga gwamnatin mulkin sojan kasar.

Karin Bayani: Fada ya sake barkewa a arewacin Mali

Haka dai na zama wata nasara ga gwamnatin mulkin sojan kasar ta Mali wadda ta kwace madafun ikon kasar a shekara ta 2020. Ita dai kasar ta Mali da ke yankin yammacin Afirka tana fama da matsalolin tsaro daga kungiyoyin daban-daban musamman cikin ynakunan arewacin kasar.