1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Dakarun MDD sun fice daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 25, 2024

Gwamnatin Kinshasa ce ta umarce su su bar kasar sakamakon gaza yin katabus wajen kawo karshen rikicin

Hoto: Wang Guansen/Xinhua/picture alliance

Majalisar Dinkin Duniya ta rufe babban ofishinta na Lardin Kivu a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, yayin da take ci gaba da janye dakarunta daga kasar, sakamakon kazancewar rikici.

Karin bayani:Dakarun SADC sun tunkari 'yan tawayen M23

Dakarun farko na wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun fara isa Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a shekarar 2003, amma yanzu haka dakaru dubu goma sha biyar ne suka fara ficewa daga kasar, bayan da gwamnatin Kinshasa ta umarce su su bar kasar, sakamakon gaza yin katabus wajen kawo karshen rikicin.

Karin bayani:Ukraine ta kaddamar da ofisoshin jakadancinta a nahiyar Afirka

Tun a karshen shekarar 2021 ne yankin arewacin Kivu ke fama da hare-haren 'yan tawayen M23 masu samun goyon bayan kasar Rwanda, inda suka kwace iko da mafi akasarin yankin.