Dakarun Najeriya sun ceto mutum 241
May 29, 2020Talla
Mai magana da yawun sojin kasar John Enenche ya ce daga cikin wadanda aka kubutar 136 yara ne sai mata 105, kuma an kubutar da su ne yayin wani sumame da sojoji suka kai kauyen Mudu da ke arewa maso yammacin jihar Borno a yakin da suka daura da 'yan ta'adda musamman ma 'yan kungiyar Boko Haram.
A wannan aiki jami'an tsaron sun yi nasarar kashe mayakan na Boko Haram goma sha biyu. Mutane 241 da aka kubutar da su daga hannun mayakan na karbar kulawa ta musamman daga jami'an kiwon lafiya.