Dakarun Pakistan sun kai hari kan wani sansanin ƙungiyar al-Qaeda.
October 30, 2006Sojojin Paikstan, tare da jiragen sama masu saukar ungulun rundunar mayaƙan saman ƙasar, sun kai hari da sanyin safiyar yau, kan wani sansanin da suka ce na horad da mayakan ƙungiyar al-Qaeda ne, a arewa maso yammacin ƙasar kusa da iyakanta da Afghanistan. Wasu jami’an hukumar sojin Pakistan ɗin sun ce, jiragen saman sun harba rokoki ne kan wata makarantar addinin islama kusa da garin Khar, babban garin da ke lardin ƙabilu na Bajur, inda ake zaton gun ba da horo ne ga wasu mayaƙan al-Qaedan su kusan 70 zuwa 80. Wannan harin dai ya zo ne kwana biyu, bayan da ’yan ƙabilun yankin kusan dubu 5, masu nuna goyon baya ga ƙungiyar al-Qaeda, suka yi zanga-zangar nuna ƙyama ga Amirka da manufofinta, a ƙauyen Damadola. A nan ne dai a cikin watan Janairun wannan shekarar, jiragen saman yaƙin Amirka suka kai hari, wai don fatattakar mataimakin shugaban al-Qaedan, Ayman al-Zawahiri, inda suka halakad da fararen hula da dama, amma ba tare da cim ma burinsu ba.