SiyasaUkraine
Rasha na kara matsa lamba a gabashin Ukraine
August 23, 2025
Talla
A cikin wata sanarwa da ta watsa ta kafar Telegram, ma'aikatar tsaron Rasha ta ce kauyukan biyu da aka kwace sun hada da Sredneïe da Kleban-Byk, kuma hakan zai share wa sojojin kasar hanyar nausawa zuwa birnin Kostyantynivka da ke da matukar mahimmanci ga dakarun Ukraine.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake fatan shirya ganawa a tsakanin shugaban Putin na Rasha da takwaransa Zelesky na Ukraine kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya sanar domin sasanta rikin kasashen biyu cikin ruwan sanhi.
Sai dai a jiya Juma'a ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya zargi shugaba Zelensky da yin zagon kasa ga shirin ganawar washegarin makamancin irin wannan zargi da Kiev ta yi Moscow.