1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai harin rokoki a Azovstal

Abdul-raheem Hassan
May 3, 2022

Duk da rahotannin da ke cewa daruruwan fararen hula na makale a tashar jiragen ruwa da ke birnin Mariupol, sojojin Rasha sun kaddamar da sabbin harin rokoki a kamfanin mulmula karafa na Azofstal da ke birnin.

Pro russische Truppen Ukraine Krieg Azovstal
Hoto: ALEXANDER ERMOCHENKO/REUTERS

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da jagoran 'yan adawa a Jamus mai ra'ayin mazan jiya Friedrich Merz, ya nufi Kiev babban bibnrin kasar Ukraine bayan da Shugaban gwamnatin Jamus Chancellor Olaf Scholz ya soke ziyararsa.

Shugabannin Ukraine sun koka kan jan kafar da Jamus ke yi na tsawon makonni wajen raba gari da gwamnatin Moscow, kuma sun soki kasar kan yadda take nuna shakkun na kai agajin manyan makamai zuwa Ukraine domin yakar sojojin Rasha.

Matakin hukumomin gwamnatin kyiev na kin maraba da ziyarar shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier a baya-bayan na, ya kara dagula alaka tsakanin kasashen guda biyu.