Dakarun RSF a Sudan amince da kudurin sulhu
November 7, 2025
Sanarwar ta biyo bayan kwace muhimmin garin El-Fasher da dakarun na RSF suka yi, wanda ya kori sojojin gwamnati daga tungarsu ta karshe a yammacin Darfur.
Tuni dai ake zarginsu da aikata kisan kiyashi da sace-sace da cin zarafin mata bayan karbe ikon da garin, kazalika a kwanakin baya-bayan nan an ga yadda suka karkata zuwa yankin Kordofan da ke makwabtaka da su, inda ake ci gaba da gwabza kazamin fada.
Gwamnatin da ke samun goyon bayan soji ba ta ce uffan ba game da sanarwar ta RSF. Tun a ranar Larabar da ta gabata, babban hafsan sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya ce dakarunsa na ci gaba da fafutukar fatattakar abokan gaba.
Sama da shekaru biyu aka kwashe ana gwabza kazamin yaki a Sudan wanda ya samo asali daga rikicin shugabanci ya hallaka mutane da dama tare da raba dubbai da matsugunnensu.
Karin Bayani:Amurka ta kudiri aniyar kawo karshen yakin Sudan