Dakarun RSF sun kashe kananan yara a Sudan
December 6, 2025
Talla
Ana ganin cewa ta yiwu alkalumman wadanda suka mutu a harin na jihar Kordofan ya karu, sai dai rashin hanyoyin sadarwa a yankin ya haifar da tsaikon ba da rahoton. A cewar wakilin Asusun Kula da Kanana Yara na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, Sheldon Yett, kashe yara kanana a markatanta babban laifi ne na take hakkin yara.
Ya kara da cewa, bai kamata a ce yara ne ke shan ukubar sakamakon rikicin ba. UNICEF ta bukaci dukannin bangarorin su mayar da wukakensu cikin kube nan take. Daruruwan fararen hula ne aka kashe a Kordofan a makwannin baya-bayan nan, yayin da fada ya koma yankin daga Darfur, bayan da mayakan RSF suka karbe iko da birn el- Fasher.