Dakarun Siriya sun sake kutsawa birnin Hama
July 31, 2011![](https://static.dw.com/image/15147392_800.webp)
Rahotanni daga Siriya na nuni da cewar da sanyin safiyar yau ne Tankokin soji sun kutsa birnin Hama, bayan mamayar da suka yi na sama da wata guda sakamakon zanga-zangar adawa mafi girma da al'ummomin yankin ke gudanarwa. Wani likita mazaunin garin na Hama wanda yaƙi a faɗi sunansa, ya shaidar da cewar kutsen sojin ya kashe a kalla mutane 17 har da wani matashi mai suna Fares al-Naem. Ya ce sojojin gwamnatin na Siriya na kai hare-hare daga kusurwowi huɗu na garin, da manyan makamai. Shugaba Bashar al-Assad dai ya kokarin dakatar da zanga-zangar adawa da mulkinsa na shekaru 11, wanda ya ɓarke tun a watan Maris, sakamakon boren neman sauyi daya faro daga ƙasashen Masar da Tunisiya wanda kuma ke cigaba da gudana a ƙasashen larabawan.Tuni dai hukumomin Siriya suka kori 'yan jaridar ketare daga ƙasar, batu dake kawo cikas a dangane da sahihancin rahotanni da ake samu daga wannan ƙasa.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdullahi Tanko Bala