1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Sojin Isra'ila sun yi wa Kudancin Gaza ruwan bama-bamai

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 11, 2023

Tun daga Lahadi sojin Isra'ila suke yi wa yankin Khan Yunis na Gaza luguden wuta har zuwa Litinin din nan, tare da ci gaba da laluben maboyar mayakan Hamas

Hoto: Leo Correa/AP Photo/picture alliance

Dakarun Sojin Isra'ila sun yi wa Kudancin Gaza kawanya tare da sakin ruwan bama-bamai a Litinin din nan, duk kuwa da gargadin da kungiyar Hamas ta yi na cewa babu wani 'dan Isra'ila da ke hannunta da zai tsira da ransa, matukar ba a amince da bukatunta kan musayar fursunoni ba.

Karin bayani:An gaza kada kuri'ar amincewa da dakatar da yakin Gaza a MDD

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito cewa tun daga Lahadi sojin Isra'ila suka yi wa yankin Khan Yunis na Gaza luguden wuta har zuwa Litinin din nan, tare da ci gaba da laluben maboyar mayakan Hamas da wasu kasashen yamma suka ayyana a matsayin ta ta'addanci.

Karin bayani:Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kwamitin tsaro daukar mataki kan Isra'ila a Gaza

A Lahadin nan aka jiyo Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres na sukar lamirin Amurka tare da da zarginta da yi wa kwamitin tsaron majalisar zagon kasa, sakamakon kujerar na ki da ta hau ta kuma murkushe matakin ganin an cimma duk yarjejeniyar tsagaita wuta a kan rikicin Gaza din da kwamitin ya amince.